<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>311</hymn_number>
<title>Duniyan Nan Ba Gaskiya, Duniya Tana Wucewa LW311</title>
<lyrics>[V1]
 1) Duniyan nan ba gaskiya, duniya tana wucewa,
 Mu, Sama mu ke so.

[V2]
 KORUS
 Can za mu yi murna, murna, murna, murna.
 Can Sama da murna, murna, murna, har abada.

[V3]
 2) Nan wahala mu ke sha, nan kuwa babu daɗewa,
 A can ba haka ba.
 Korus

[V4]
 3) Halin duniyan nan mu ƙi. Mu, bin Yesu mu ke yi
 A duniyan nan yanzu.
 Korus

[V5]
 4) Yabon Yesu mu ke yi, Ubangijinmu ne shi,
 Can za mu gan shi kuwa.
 Korus

[V6]
 5) Can fa daɗi za mu ji, yabon Yesu za mu yi,
 Yesu Mai Cetonmu.
 Korus</lyrics>
</song>